Jam’iyyar APC a karamar hukumar Hadejia ta zabi shugabannin da za su jagorance ta

0 232

Jam’iyyar APC a karamar hukumar Hadejia ta zabi shugabannin da za su jagoranci harkokin jam’iyyar a tarukan jam’iyyar na kananan hukumomi da aka kammala.

Da yake jawabi, wakilin APC na jiha, Alhaji Sadisu Tabara Gumel ya yaba da yadda aka gudanar da zaben.

A nasa jawabin Shugaban Karamar Hukumar Hadejia Alhaji Abdulkadir Umar Bala T.O ya hori zababbun shugabannin da suyi aiki tukuru domin fuskantar kalubalen babban zaben 2023.

Wadanda aka zaba sune Alhaji Magaji Munkaila, Shugaba; Yawale Musa Kawaki, Mataimakin Shugaba; Baba Sani Muhammad, Sakatare da Yusuf Muhammad Tama, Ma’aji.

Sauran su ne Yahaya Ahmed, Jami’in Hulda da Jama’a; Muhammad Musa, Shugaban Matasa da Hajia Jimmai Sani, Shugabar Mata.

Jam’iyyar ta kuma sanar da sunayen wakilan jihohi 5-5 a kowace mazaba da wakilai na kasa guda uku da suka hada da Architecture Aminu Kani, Alhaji Salisu Zakar da Alhaji Hussaini Muhammad Rally.

Leave a Reply

%d bloggers like this: