Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta kubutar da mutane 9 da akayi safarar su a jihar Jigawa

0 110

Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta kubutar da mutane 9 da akayi safarar su a jihar Jigawa.

Kwanturola na jiha, Isma’il Abba Aliyu ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske a ofishinsa, da ke Dutse babban birnin jihar.

An kubutar da su ne a yayinda ake kokarin tsallakawa da su zuwa Jamhuriyar Nijar, domin kaisu Libya, da kuma kasashen Turai.

Ya bayyana cewa 6 daga cikin wadanda aka kashe mata ne yayin da ragowar ukun maza ne, yan tsakanin shekarun 20 zuwa 29.

Aliyu ya ce za a mika wadanda abin ya shafa ga hukumar NAPTIP don ci gaba da bincike.

Ya kuma shawarci iyaye da sauran jama’a da su guji masu yaudarar dake yaudarar su, da nufin tura ‘ya’yansuzuwa kasashen waje da sunan aikatau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: