Jam’iyyar APC mai mulki ta kasa ta karyata labarin da ake yadawa cewa tana zawarcin tsohon shugaban kasa GoodLuck Jonathan

0 118

jam’iyyar APC  mai mulki ta kasa ta karyata labarin da ake yadawa cewa ta bawa tsohon shugaban kasa GoodLuck Jonathan tikiti kai tsaye na tsaya mata Takara a 2023, wanda ake ta yada jitajitar cewa yana shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Jam’iyyar ta kara da cewa, dukwanda ya dawo jam’iyyar yanada damar tsayawa Takara a kowanne mataki a karkashin tutar jam’iyyar.

Shugaban kwamitin tsare tsare na rikon kwaryar Jam’iyyar na kasa Senator John James  ne ya bayyana hakan cikin wata takarda daya rabawa manema labarai a yau Juma’a a babban birnin tarayya Abuja.

Ya kara da cewa babu wani wanda suka bashi tikitin tsayawa Takara a cikin wadanda suka koma jam’iyyar, ya kara da cewa anyiwa kalamansa mummunar Fahimta ne, akan cewa za’adagawa wasu da suka koma jam’iyyar kafa.

James cikin bayanansa ya tabbbatar da cewa kafin mutum ya zama wanda zaiyiwa jam’iyyar Takara sai ya cika shurudanta da kuma tabbatar da yaci zaben fidda gwanin da za’agudanar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: