“Akwai bukatar a rika yin gwajin shan kwayoyi kafin a bawa mutane shaidar girmamawa” Farida Waziri

0 96

Tsohuwar Shugabar Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa Misis Farida Waziri, ta ce akwai bukatar a rika yin gwajin shan kwayoyi kafin a bawa mutane shaidar girmamawa.

Misis Farida Waziri ta bayyana hakan ne lokacin da take tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Abuja.

An nada Farida Waziri a matsayin mamba a Kwamatin Bada Lambar Girmamawa ga mutanen da suke ciyar da kasa gaba.

Kwamatin shine yake da Alhakin zabar Mashahuran yan Najeriya da sukayi shuhura wajen bawa kasar na gudunmawa.

A cewarta, gwajin shan kwayoyin zai yi daidai da manufar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaki da shan miyagun kwayoyin, kamar yadda ya kaddamar da daftarin hakan a ranar 26 ga watan Yuni na shekarar 2021.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya rawaito cewa Ministan Ayyukan na Musamman Sanata George Akume, shine ya kaddamar da Kwamatin.

Mai Martaba Sarkin Lafiya Justice Sidi Muhammad 1 (retd), shine shugaban Kwamatin, Mrs Farida Waziri (North-Central), Muhammed Ja’afaru (North-West), Alhaji Sali Bello (North-East), Chief Inikio Dede (South-South) and Prof. Lazarus Ekwueme (South-East).

Leave a Reply

%d bloggers like this: