Majalissar wakila ta Najeriya tayi kira ga gwamnatin tarayya akan ta kawo karshen cutar amai da gudawa a jihar Jigawa da sauran jihohi

0 75

Majalissar wakilan tarayyar kasar nan tayi kira ga gwamnatin tarayya akan ta kawo karshen cutar Amai da gudawa a jihar Jigawa da sauran Jihohin dake fama da wannan cutar.

Majalissar ta kuma bukaci kwamitinta dake kula da fannin lafiya akan su hada hannu da ma’aikatar lafiya ta kasa da sauran hukumomin lafiya domin bulla da hanyoyin da za’a magancewa yan kasar nan wannan cutar.

Wannan cigaban ya biyo bayan kudirin da dan majalissa mai wakiltar kananan hukumomin Kaugama da Malam Madori Abubakar Makki Yalleman ya shigar ne a zauran majalissar.

Cikin bayanan Elleman ya bukaci ma’aikatar lafiya ta bullo da hanyoyin da za’a magance wannan matsalar da wasu matsalolin lafiya da ake fuskanta a mazabarsa.

Ya kara da cewa cikin wata 1 daya gabata ansamu kimanin mutane 2,000 da suka kamu da wannna cutar a fadin kasar nan tare da rasa rayuka 30.

Maki Elleman cikin bayanansa ya kara da cewa cutar amai da gudawa ba cutar bace da za’ayi wasa da ita ba, inda yace cikin watanni 4 da suka gabata yawan wadanda suka kamu da wannan cutar a kasar nan yakai mutum dubu 10 tare da asarar rayuka 295 mafi akasari ana Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: