Jamiyyar APC reshen karamar hukumar Kazaure ta kaddamar da kwamiti mai wakilai bakwai domin binciken zarge zargen da ake yiwa wakilin mazabar tarayya ta Kazaure Muhammad Gudaji Kazaure wanda jamiyyar ta dakatar na tsawon watanni shida

Shugaban kwamitin riko na jamiyyar APC na Kazaure Hassan Lawan ya kaddamar da kwamitin a sakatariyar jamiyyar dake Kazaure

Yace aikin kwamitin ya hadar da yin bincike kan lefukan daya aikata da kuma bada shawara kan hukuncin da ya kamata a dauka akansa

Mallam Hassan Lawan ya kara da cewar an baiwa kwamitin kwanaki goma domin gabatar da rahotansa

Kwamitin yana karkashin jagorancin Mukarrabu Hamza da Alhaji Sanusi Lawan Sakatare

Sauran wakilan kwamitin sun hadar da Yusif Bala Gizo da Mansir Tafida da Yusif Mai Takalma da Abdullahi B Garba da Sani Yahaya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: