Jam’iyyar PDP ta yi allawadai da dakatar da Sanata Natasha daga majalisar dattawa

0 108

Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP ta yi allawadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa bayan zargin shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio da cin zarafinta.

Jam’iyyar ta bayyana takaicinta kan yadda a cewarta aka yi gaggawar dakatar da Natasha, “ba tare da an gudanar da binciken ba sani ba sabo ba kan zargin da ta yi wa shugaban majalisar.”

Wannan jawabin na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa Debo Ologunagba, ya fitar, inda ya ce majalisar tana “amanna tare da rufa-rufa domin ba mai laifi kariya.”

“Dakatar da ita na wata shida hana mutanen Kogi ta Tsakiya wakilci ne, wanda haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya ba su.”

PDP ta ce kamata ya yi shugaban majalisar ya kare kansa daga zargin ta hanyar sauka daga jagorantar zaman tattauna batun, kasancewar shi ake zargi matuƙar “babu wani da yake ɓoyewa. Wannan ba ƙaramin abin kunya ba ne ambaton shugaban majalisar dattawa zarginsa da cin zarafi, wanda ɓata sunan majalisar ne baki ɗaya.”

Leave a Reply