Za a zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga kan wani mutu da ake tsare da shi a wani gidan yari da ke jihar South Carolina ta Amurka, bayan samun shi da laifin kashe iyayen budurwarsa ta hanyar dukan su da sanda.
Mutumin zai kasance na farko da aka kashe ta wannan tsari a cikin shekara 15.
A lokacin zartar da wannan hukunci kan mutumin mai suna Brad Sigmon a yau Juma’a da ƙarfe 11:00 na dare a Amurka, maharba uku riƙe da bindiga za su harbe shi a lokaci guda a kan ƙirjinsa ta hanyar amfani da wasu alburusai na musamman.
Tsarin aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar bindiga ya tanadi cewa za a ɗaure mutumin ne a kan kujera a cikin ɗakin zartar da hukuncin, inda kuma za a sanya alamar wurin da za a harba a daidai ƙashin zuciya.
An samu Sigmon, mai shekara 67 a duniya da laifin kisan iyayen budurwarsa David da Gladys Larke a shekarar 2001, kafin yin garkuwa da ita budurwar tasa.
Daga baya ta samu tsira daga hannun shi yayin da ya bi ta da harbi.
Duk da cewa an bai wa Sigmon zaɓin hukunci ta hanyar lantarki ko kuma allurar mutuwa, lauyansa ya ce ya zaɓi hanya mafi tsanani ne kasancewar bai yarda da aikin sauran hanyoyin biyu ba.
Shi ne zai zama mutum na farko da za a zartar wa hukuncin kisa ta hanyar harbin bindiga tun shekara ta 2010, kuma zai kasance mutum na huɗu da aka taɓa zartar wa hukuncin ta wannan hanya tun bayan da Amurka ta dawo da aiwatar da hukuncin kisa a 1976.
– BBC Hausa