Hukumar FBI ta kama wani soja a Amurka bisa zargin sayar da bayanan sirri ga wasu mutane a China, kamar yadda Ma’aikatar Shari’a ta kasar ta bayyana.
Sojan mai suna Jian Zhao, wanda ke aiki a wani sansanin soja a jihar Washington, ana zarginsa da satar kwakwalwar kwamfuta da wasu kayayyakin gwamnati tun daga watan Yuli na shekarar 2024, inda ya karɓi akalla dala dubu 15 a matsayin biyan kuɗi.
Zhao da wasu abokan aikinsa biyu, Li Tian da Ruoyu Duan, ana tuhumar su da aikata laifukan cin hanci, da sata da kuma mika bayanan tsaro ga waɗanda ba su da alhakin sani.
Babbar Mai Shari’a ta Amurka, Pam Bondi, ta ce an kama mutanen ne bisa zargin cin amanar kasa da rage karfin tsaron Amurka, tana mai cewa za su fuskanci hukunci mai tsauri.