An fitar da sunayen mutane da kungiyoyi 17 da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci a Najeriya

0 155

Kwamitin Hukunta Wadanda Ke Da Alaka da Ta’addanci a Najeriya ya fitar da sunayen mutane da kungiyoyi 17 da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci.

Sunayen sun hada da Simon Ekpa, da Godstime Promise Iyare, da Francis Mmaduabuchi da wasu mutane daga sassa daban-daban na kasar nan.

A cewar wata sanarwa daga kwamitin, lissafin an tantance shi ne bisa shawarar Antoni Janar na Tarayya, kuma Shugaban Kasa ne ya amince da shi.

Hakan na nufin an umarci bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su daskarar da duk wasu kadarori da asusun ajiyar kudaden wadannan mutane da kungiyoyi ba tare da gargadinsu ba, tare da mika rahoto ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC.

Leave a Reply