Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga yankin Kogi ta bayyana aniyarta ta shigar da kara kan dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi mata na tsawon watanni shida, sakamakon sabanin da ta samu da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan batun zaman kujera.
Lauyanta, Victor Giwa, ya ce dakatarwar ba ta da dalili saboda akwai umarnin kotu da ya hana Majalisar ɗaukar mataki a kan lamarin kafin sauraron karar da ke gabanta.
Sanatar ta sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya domin kare hakkinta, tana mai cewa an ci zarafinta ta hanyar neman yin lalata da ita abin da Akpabio ya musanta.
Majalisar ta bayar da sharadin cewa za a rage wa’adin dakatarwar ne kawai idan ta rubuta takardar neman afuwa ga Shugaban Majalisar.