Jam’iyyar PDP zata kammala babban taronta a karshen watan Oktoba

0 93

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP sun bayyana kyakkyawan fatan cewa jam’iyyar za ta kammala babban taronta na kasa na ranar 30 ga watan Oktoba cikin hadin kai.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, shine ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi bayan ganawarsu jiya a Abuja.

Gwamna Tambuwal ya ce jam’iyyar a shirye take ta samar da dandalin da ake bukata wanda ‘yan Najeriya da dama za su iya cimma burinsu na siyasa.

Ya kara da cewa ana cigaba da gudanar da shirye-shiryen babban taron domin jam’iyyar ta samu nasarar gudanar da babban taronta, cikin kwanciyar hankali da lumana.

Da yake amsa tambayoyi dangane da halatar dan takarar da aka amince da shi a Arewa domin shugabancin jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, da mai neman sakataren jam’iyyar na kasa, Samuel Anyanwu, a wajen taron, Gwamna Tambuwal ya ce sun zo ne don tattaunawar sirri, ba wai neman a mara musu baya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: