Jarirai 11 sabbin haihuwa sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Tivaouane da ke yammacin kasar Senegal

0 67

Jarirai 11 sabbin haihuwa sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani asibiti a birnin Tivaouane da ke yammacin kasar Senegal.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce gobarar ta tashi a sashen haihuwa na asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh.

A cewar ‘yan siyasar Senegal, rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki.

Magajin garin, Demba Diop Sy ya ce an ceto jarirai uku daga gobarar.

Dipo Sy ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa gobarar ta bazu cikin sauri kuma har yanzu jami’an bayar da agajin gaggawa na wajen.

Ya ce ana gudanar da bincike kuma zai katse bulaguron da yayi domin komawa Senegal cikin gaggawa.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kan halin da ake ciki a fannin kiwon lafiyar kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: