Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami musamman a lokacin gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam da ya rabawa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Sale Tafida, ya bukaci ‘yan siyasa da su shawarci mabiyansu da su guji yin hakan, su kuma bi ka’idojin gudanar da zabe.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kame duk wanda ke son yin amfani da zaben wajen tada fitina da karya dokar da ke kunshe a cikin dokokin zabe.

A saboda haka, Aliyu Tafida ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal da kuma yin amfani da ka’idojin da aka tanada domin samun sahihin zaben fidda gwani a jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: