Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya yi maraba da cigaban da aka samu na bayyana jihar a matsayin mafi sauki wajen gudanar harkokin kasuwanci a kasarnan.

Gwamnan yana mayar da martani ne kan yadda jihar ta kasance ta farko a cikin jihoshin da suka samar da kyawawan yanayi wanda zai bunkasa kasuwanci a Najeriya.

Wannan ya na kunshe ne a rahoton gudanar da kasuwanci cikin sauki da aka fitar, wanda kwamitin kula da yanayin kasuwanci na shugaban kasa ya gudanar da bincike dangane da halin da ake ciki game da kyakyawan yanayin kasuwancin jihoshi na kanana da matsakaitan masana’antu.

Jihar Gombe tana gaba da jihohin Sakkwato da Jigawa da Akwa Ibom wadanda suka zo na 2 da na 3 da na 4.

Dangane da cigaban, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya ce samun wannan nasarar ya nuna  karara irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen samar da shugabanci nagari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: