Yadda wasu fusatattun matasa sun lakadawa wani mai shekaru 40 duka har ya mutu a Jigawa.

0 118

Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce wasu fusatattun matasa sun lakadawa wani mai shekaru 40 da ake zargin barowa ne, Hassan Sale, dukan kawo wuka da yayi ajalinsa a jiharnan.

Kakakin rundunar ‘yansanda na jiha, Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai yau a Dutse.

Shisu Adam ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyen Chandan da ke karamar Hukumar Birnin Kudu lokacin da wanda ake zargin ya yi kokarin kutsawa cikin shagon sayar da kayayyaki.

Marigayin ya shiga hannun mai shagon ne, wanda yayi masa ihun da ya jawo hankalin mazauna kauyen.

An lakada masa kazamin duka inda aka garzaya da shi zuwa babban asibitin Birnin Kudu don kula da lafiyarsa amma ya mutu yayin da yake karbar magani a ranar 14 ga Yuni.

Kakakin na yansanda yace ana cigaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: