Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau ya umarci sojoji da su kara kaimi wajen yaki da rashin tsaro.

0 128

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau ya umarci sojoji da su kara kaimi wajen yaki da rashin tsaro.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin rundunar hadin gwiwa a barikin Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ya tabbatarwa da sojojin karin samar da kayan yaki.

Buhari ya isa filin faretin barikin na Maimalari da misalin karfe 11 da rabi na safe kuma ya samu tarba daga gamayyar sojoji da ‘yan sanda.

Daga nan ya gaggauta tafiya, inda ake kula da sojojin da suka ji rauni inda ya jajanta musu tare da yi misu tambayoyi masu yawa.

Tun da farko, a jawabinsa na marabarsa, mukaddashin kwamandan gidan operation Hadin Kai da ke yaki da masu tayar da kayar baya, Manjo Janar Omogwui, ya bayyana ziyarar a matsayin ta musamman wacce zata karfafa gwiwa ga sojojin dake filin daga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: