Jigawa ta rike matsayin adalci wajan kaddamar da kasafin kudi a 2020.

0 195

Gwamnatin Jihar Jigawa ta rike matsayin ta a cikin Jihohin kasar nan 36  na wadanda suka fi yin adalci wajan kaddamar da kasafin kudi a 2020.

An bayyana hakan ne Cikin wani bincike da aka gudanar wanda aka kaddamar a dakin taro na Ladi Kwali dake babban birnin tarayya Abuja

Yayin gudanar da binciken na 2018, an gano cewa jihar Jigawa na da kaso 83 cikin dari na gabatar da kasafin kudin ta, yayinda a 2020 jihar Jigawa ta aiwatar da kasafin kudaden ta da kaso 90 cikin 100. Hakkan ne yasa hukumar dake bibiyar kasafin kudade da aiwatar da su ta kasa ta jinjinawa gwaman Muhammad Badaru Abubakar da sauran tawagar gwamnatin sa bisa sake rike mukamin sa na gwamnatin  da ta fi aiwatar da kasafin kudin ta kamar yanda ta alkawarantawa al,umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: