

Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar sake gina hanyar Kafin Hausa zuwa Jahun zuwa Ajinge zuwa Gaya akan kudi naira miliyan dubu ashirin da biyar.
An bada aikin kwangilar ne ga kamfanin H and M da nufin kammalawa a shekaru biyu da rabi.
Injiniya mai kula da aiyukan kamfanin, Injiniya Muhammad Sarkina ya sanar da hakan a lokacin da gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya ziyarci wurin aikin.
- Why price of cement is high? -Dangote
- Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Ya Yiwa Gwamna Badaru Ta’aziyar Rasuwar Dan Uwansa
- Za A Yi Kididdigar Masu Aikin Karuwanci A Bauchi
- Kuji tsoron Allah ko koma gare Shi, Atiku yayi kira ga yan Najeriya.
- Goodluck Jonathan: Kuri’un talakawa ya kamata su tattance zabe ba kotu ba
Ya kuma yiwa gwamnan bayanin matsayin ayyukan.
A jawabinsa, Gwamna Badaru Abubakar ya yaba da yadda aikin ke gudana tare da fatan za a kammalashi akan lokaci.
Gwamna Badaru Abubakar ya kara da cewar gwamnatin tarayya ta gudanar da ayyuka a jihar Jigawa da suka hadar da ayyukan hanyoyi dana ilmi da aikin gona da kuma bunkasa tattalin arziki.