Jawabin Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje kan bahaya a bainar jama’a

0 99

Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje CON, ya jaddada cikakken hadin kai da goyon bayan sarakuna wajen tabbatar da samun nasarar shirin yaki da bahaya a bainar jama’a a kowanne mataki.

Mai Martaba Sarki, ya bada wannan tabbaci ne a jiya lokacin da ya karbi wata tawaga ta kwamatin aiwatar da shirin a jihar nan, wadda kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa na jiha Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa ya ke jagoranta wadda suka ziyarci fadar sarkin.

Mai Martaba Sarkin wanda shine shugaban majalisar sarakunan jihar Jigawa, ya umarci hakimai da dagatai da masu unguwanni dake masarautarsa da su fadakar da jama’a game da illolin bahaya a bainar jama’a. Tun da farko, kwamishina yace sun ziyarci fadar ne domin sanar da mai Martaba Sarki al’amuran da suka jibinci aiwatar da shirin yaki da bahaya a bainar jama`a, a kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa da kuma Birniwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: