Jihar Jigawa ta kaddamar da biyan hakkokin magadan maa’ikatan da suka rasu a bakin aiki Naira miliyan 213 da dubu 665
Asusun adashen gata na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa ya kaddamar da biyan hakkokin magadan maa’ikatan da suka rasu a bakin aiki da kuma cikon kudaden fansho ga magadan masu fansho da suka rasu, wanda ya tasamma naira miliyan 213 da dubu 665.
Babban Akanta na asusun, Mallam Kamilu Aliyu Musa ya sanar da hakan yayin kaddamar da aikin biyan a gidan ‘yan fansho a Dutse, a madadin sakataren zartarwa na asusun Alhaji Hashim Ahmed Fagam.
Yace za a biya hakkin mamata ga magadansu a matakan jiha da kananan hukumomi da kuma sashen ilimi na kananan hukumomi.
Daga nan ya yabawa gwamnatin jiha bisa goyon baya da hadin kan da take bawa asusun a kowane lokaci.