Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da kwangilar gyare-gyare a makarantar sikandiren hadaka ta Malam-Madori a kan kudi fiye da naira miliyan 100.

Kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha na jiha Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya bayyana haka lokacin daya kai ziyara makarantar a cigaba da rangadin duba makarantun sakandiren kwana da yake yi a fadin jiharnan.

Yunusa Danzomo ya ce kasancewar gwamnati mai ci ta baiwa harkokin ilimi fifiko ya sa gwamnati ta dukufa wajen gyara gine-gine a makarantu domin samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.

Kwamishinan wanda ya ziyarci makarantun sikandiren kwana a shiyyoyin ilimi na Hadejia da Gumel, ya bayyana gamsuwa bisa goyan bayan masu Martaba Sarakuna ga kwamitocin kula da harkokin ilimi na makarantu da kungiyoyin iyayen yara da Malamai da hukumomin tsaro wajen samar da ilimi mai inganci da kuma tsaro a makarantun jiharnan.

Ya baiwa shugabannin makarantun tabbacin duba bukatun su domin cigaban ilimi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: