Jihohi 28 ne zasu fuskanci Ambaliyar Ruwa a wannan shekarar, harda Jigawa

0 65

Kimanin Jihohi 28 ne zasu fuskanci Ambaliyar Ruwa a wannan shekarar, kamar yadda Ministan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa Engineer Suleiman Adamu ya sanar.

Ministan ya bayyana hakan ne a taro kan Nazarin Ambaliyar Ruwa a shekarar 2021, wanda hukumar Lura da Yanayi ta Kasa ta shirya, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN.

A cewarsa cikin Jihohin da za’a samu ambaliyar ruwan sun hada da Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi. 

Sauran Jihohin sune Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba and Zamfara states. 

Ministan ya ce ambaliyar ruwan da aka samu a shekarar 2012, ta haifar da asarar rayuka da kuma lalata dukiyoyi masu tarin yawa a kasar nan.

Kazalika, ya bayyana cewa fadawa mutane halin da ake ciki ya zama dole domin su fara daukar matakan dakile matsalar ambaliyar a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: