Mahukunta sun hana sallar idi a kasar Ghana

0 84

Hukumomin kasar Ghana sun bayar da sanarwa cewa ba za a yi Sallar Idi ba a fadin kasar baki daya.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar shugaban limaman kasar suka fitar sun ce ana tunawa kowa cewa annobar korona har yanzu ba ta bar cikin al’umma ba, don haka dokokin da aka sanya saboda annobar haryanzu suna nan.

Sanarwar ta shaida wa duka limaman kasar cewa a gabatar da Sallah Idi a masallatan Juma’ar kasar maimakon zuwa masallatan da aka tanada domin gabatar da Sallar Idin.

Yayin Sallar sharudan da aka sanya a baya dole a bisu yanzu:

Dole ne kowane masallaci ya sanya takunkumin fuska.

Wajibi ne a samar da dokiti da ruwan wanke hannu da kuma sinadarin sanitaiza.

Kuma ko wane masallaci ya je masallaci da daddumarsa ko tabarmarsa.

Dole a rika ba da tazara da kuma samar da sinadarin duba yanayin zafin jikin duka masallatan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: