Yan bindiga: An afkawa ofishin ‘yan sanda tare da kashe mutum biyu

0 89

Wasu ‘yan bindiga suk kai hari wani ofishin ‘yan sanda a Obosi da ke Karamar Hukumar Idemili ta arewa a jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.

Yan bindigar sun kona ofishin tare da kashe mutum biyu.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Chris Owolabi ya ce komai ya koma yadda yake a Obosi kuma suna ci gaba da neman ‘yan bingidar.

Kuma ya bai wa ma’aikatansa umarnin a duba duk wani lungu da sako domin nemo masu laifin.

Babu dai wanda ya san ya aka yi ‘yan bindigar suka afkawa wannan ofishi sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: