Jimillar yara sama da miliyan 18 ne basa zuwa makaranta a Najeriya

0 65

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya  bayyana damuwa bisa yadda kididdiga ke nuna cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ya kai miliyan 18 da rabi, kuma yana ci gaba da hauhawa.

Shugaban asusun a jihar Kano, Rahama Farah, wanda ya bayana haka a wata tattaunawa da ‘yan jarida a kan shirin ilimin ‘yaya mata ya ce daga cikin yara  miliyan 18 da dubu dari 5 din, miliyan 10 mata ne, wanda yake a mastayin kaso 60 na ilahirin adadin.

Ya bayyana damuwa a kan yadda kididdigar ta ta’azzara rashin daidaito a tsakanin jinsi, inda yarinya daya cikin ‘yaya mata 4 daga iyalan da basu da karfin tattalin arziki a yankunan karkara  ne kawai suka kammala karamar sakandire.

Farah ya ce hare hare da ake kai wa makarantu da wasu cibiyoyin ilimi sun taimaka wajen rage rage dauki  da yara ke yin a neman ilimi a fadin kasar, inda yace akwai yiwuwar hakan ya shafi karin ‘yaya mata fiye da maza.

Sai dai ya ce kawo dauki da asusun kula da kananan yara tare da gwamnati da sauran kungiyoyi suka yi,  ya sa yanzu yara mata miliyan 1 da dubu dari 4 sun  yi samu damar komawa makaranta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: