Jirgin Farko Na Maniyyatan Hajjin Bana A Jigawa Zai Tashi Ranar Asabar Mai Zuwa

0 78

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta tabbatar da cewa jirgin farko na maniyyata aikin hajjin bana zai tashi zuwa Saudiyya domin aikin hajjin bana a ranar Asabar mai zuwa, 27 ga watan Mayu.

Sakataren zartarwar hukumar, Alhaji Umar Labbo, shine ya sanar da haka a jiya yayin ganawa da manema labarai a Dutse.

Yace ana sa ran tashin jirgin farko na kamfanin Azman dauke da maniyyata 395 daga filin jiragen saman kasa da kasa na Dutse.

Alhaji Umar Labbo yayi bayanin cewa kawo yanzu hukumar ta kammala aikin bizar sama da alhazai dubu 1 da 500 tare da raba musu kayan sawa da sauran kayayyaki domin aikin hajjin na bana.

Ya kara da cewa hukumar ta biya naira miliyan dubu 4 ga hukumar jin dadin alhazai ta kasa, wanda ya zama kashi 100 cikin 100 na kudaden aikin hajjin maniyyatan jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: