Matatar Man Dangote Zata Samar Da Da Gurabun Aikin Yi Ga Matasan Najeriya

0 76

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatar mansa da aka kaddamar za ta samar da gurabun aikin yi ga matasan Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a Legas a lokacin kaddamar da matatar mai da karfin tace danen mai ganga 650,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Ana sa ran matatar za ta ke samar da zai fitar da man fetur, dizel, man jirgin sama da Kalanzir sauran kayayyakin da aka tace daga danyen mai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da wasu Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma ne ke halartar bikin kaddamar da matatar mai, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.

Shugabannin da suka halarci taron sun hada da Shugaban Togo, da na Ghana, Nana Akufo-Addo da na Senegal, Macky Sall, da na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, da na Chadi, Mahamat Déby da kuma wasu Jakadun kasashe da dama. Kazalika, Shugaban Rwanda, Paul Kagame, wanda bai halarci bikin kai tsaye ba, ya gabatar da jawabi ta intanet.

Leave a Reply

%d bloggers like this: