Ka dena tarawa ‘yan Najeriya tulin bashi – Gargadin Obasanjo ga Buhari

0 292

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina karbar basussuka daga kasashe da hukumomin waje saboda gwamnatinsa tana tara basussuka ga ‘yan Najeriya da za a haifa nan gaba.

Obasanjo wanda ya yi magana a ranar Lahadin da ta gabata a wani taron da aka yi a kasar Afirka ta Kudu, ya kalubalanci shirin gwamnatin tarayya na karbar sabbin basussuka daga waje, inda ya dage cewa idan aka bar basussukan da ake da su ba a biya ba, suna iya zama matsala ga gwamnatocin da za su biyo baya.

Ya kara da cewa “Gwamnatin Tarayya na tara basussuka ga ‘yan Najeriya masu zuwa, wanda hakan kuskure ne.”

Tsohon shugaban ya lura cewa bashin ba shi ne matsala ba, matsalar irin wannan dimbin bashin ita ce, rashin tsare-tsare da kuma matakan karfin biya.

Tsohon shugaban ya ce karbar bashi don yin al’amuran yau da kullum shine girman wauta ga kowace kasa, ko ma mutum daya.

“Don haka, idan muna cin bashi don al’amuran yau da kullum, hakan wauta ne. Idan kuma muna cin bashi don aiyukan cigaban da za su iya biyan kansu, wannan abu ne mai kyau. Sannan maganar biyan bashin fa, tsawon wane lokaci za a dauka kafin ya biya kansa?

“Amma muna cin bashi da tara bashi ga ‘yan Najeriya masu zuwa da masu zuwa na bayan su, wannan kuskure ne, me ye anfanin hakan. Bashin me muke ci haka?”

Leave a Reply

%d bloggers like this: