Shugaba Buhari ya mayar da kamfanin mai na NNPC a matsayin wanda zai iya ba da dama a zuba hannun Jari

0 137

Shugaba Kasa Muhammadu Buhari, a matsayinsa na Ministan harkokin man fetur ya bayar da umarnin mayar da kamfanin mai na NNPC a matsayin wanda zai iya ba da dama a zuba hannun Jari, wato Petroleum Company Limited.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina ya bayyana, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

A cewarsa, hakan ya yi dai-dai da bangare na 53(1) na Dokar Man Fetur ta 2021, wadda ta bukaci Ministan Man Fetur ya mayar da kamfanin wanda za a iya zuba jari cikin watanni 6 bayan sa hannu kan dokar.

Don haka ne Shugaba Buhari ya bukaci shugaban kamfanin, Malam Mele Kyari, ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da sauya kamfanin.

Wanda kuma Shugaba Buhari ya nada darektocin hukumar gudanarwar kamfanin.

Da suka hada Sanata Ifeanyi Ararume wanda shi ne ciyaman din hukumar gudanarwar kamfanin yayin da Mele Kolo Kyari ne shugaban hukumar sannan Umar I. Ajiya shi ne babban darektan da ke kula da harkokin kudi.

Sauran mabobin hukumar sun hada da Dokta Tajudeen Umar da Misis Lami O. Ahmed da Mallam Mohammed Lawal da Sanata Margaret Chuba Okadigbo da Barrister Constance Harry Marshal da Cif Pius Akinyelure.

Leave a Reply

%d bloggers like this: