Kananun yara 5 ne suka mutu sakamakon rashin iska a cikin motar da suka makale a jihar Neja

0 127

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar wasu kananan yara biyar sakamakon rashin iska a cikin wata mota a garin Minna, Jihar Neja.

Yaran sun hada da mata hudu da namiji daya, ’yan uwa uku da wasu biyu daga iyaye daban-daban ciki har da dan mai motar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, ofishinsu da ke Kpakungu ya samu rahoto cewa an tsinci gawar yara biyar ’yan shekara biyar zuwa 13 makale a cikin wata mota kirar Honda Civic a unguwar Gurara Albishir da ke Minna.

Abiodun ya ce an gano nunfashin yaran sun shake ya dauke ne a cikin motar, bayan da iyayensu da makwabta suka kwashe awannin suna neman su.

Ya ce daga bisani aka sanar da ’yan sanda suka ziyarci wurin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: