Karamar Hukumar Gwaram ta raba buhun-hunan masara 2,480 a mazabun yankin

0 165

Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Muhammad Dan’Asabe Sara ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da rabon masarar.

Yace gwamna Badaru Abubakar ne ya bada masarar domin tallafawa masu karamin karfi a cikin al’umma.

Alhaji Muhammad Dan’Asabe Sara yace Karamar Hukumar ce zata dauki nauyin kai masarar kowacce mazaba inda ya gargadi yan siyasa da shugabanni su guji karkatar da masarar.

A jawabinsa sakataren kwamitin rabon wanda kuma shine sakataren Karamar Hukumar, Alhaji Aminu Sa’id Kondiko yace Karamar Hukumar ta kaddamar da kwamiti domin sa’ido wajen rabon masarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: