Gwamnan babban bankin kasa CBN Mr. Godwin Emefiele, yace za’a dauki matakin fadada wasu ka’idoji da nufin shawo kan karayar tattalin arziki, kasancewar ka’idojin dake akwai a yanzu haka sun kuntata.

Ya bayyana hakan a matsayin tilas domin shawo kan durkushewar tattalin arziki da kuma karancin wadatuwar takardun kudade a hannun jama’a, matakin da kwamatin tsare tsaren kudade na bankin ya cimma a taron da ya gudanar makon jiya.

Emmefiele ya alakanta hakan da janye tallafin mai na baya bayannan, da ya haddasa hauhauwar farashinsa, da kuma kwaskwarima da da akayiwa kasuwar canjin kudi, wanda yace muddin ba’a dauki matakan da suka kamata ba, to babu shakka kalubaken karancin takardun kudaden zai tsaurara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: