Gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa maaikatar ciniki da masanaantu ta jiha kudi Naira miliyan 105 domin bada bashi ga kanana da matsakaitan masanaantu domin rage radadin cutar covid 19

Kwamishinan ciniki da masanaantu na jiha Alhaji Salisu Zakar ya sanar da hakan a wajen bikin bude taron bita na yini biyu kan sayen kayayyakin gwamnati na gaggawa karkashin tsarin covid 19 a garin Hadejia.

Kwamishinan ciniki da masanaantu Salisu Zakar Hadejia

Yace maaikatarsa tane sake nemo wasu tsare tsaren cigaba tare da hadin gwiwar wasu maaikatu da hukumomin gwamnati ciki hadda hukumar kula da kanana da kuma matsakaitan masananatu ta kasa inda za a zabo mutane 90 da kowacce karamar hukuma domin samu tallafin naira dubu hamsin kowannensu

A jawabinsa babban daraktan hukumar tantance aiyukan bada kwangila ta jiha Alhaji Ado Hussaini yace an shirya taron ne domin yiwa mahalarta taron bayani akan ka’idojin bayar da kwangila.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: