Matasa Maza da Mata 300 sun samu horo daga hukumar samar da aiyukan yi ta kasa NDE a Jigawa

0 206

Hukumar samarda aiyukan yi ta kasa NDE ta kaddamar da bada horan watanni uku ga matasa maza da maza guda dari a jihar Jigawa.

Shugaban hukumar a jihar nan Malam Abubakar Jamo ya sanar da hakan a lokacin ganawa da manema labarai a garin Dutse.

Yace wasu daga cikin matasan zasu sami horo akan bangarori daban daban na aikin gona.

Mallam Jamo ya kara da cewar ana gudanar da bada horan ne karkashin shirin bada horo a yankunan karkara.

Inda yace matasan za a tura su wuraren koyan sanin makamar aiki na makonni biyu a gonaki.

Mallam Abubakar Jamo ya shawarci matasa dasu shiga cikin shirin domin samun hanyoyin dogaro da kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: