Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya shaida wa gwamnatin jihar Sokoto cewa ya zama wajibi a kare martabar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.
Jaridar Daily Trust ta waito cewa Shettima ya faɗi hakan ne a wani taron Zaman Lafiya da Tsaro na Arewa Maso Yammacin ƙasar, wanda ake yi a jihar Katsina a yau Litinin.
Ya ce “A duk wasu batutuwa na ci gaba a ƙasar nan, ina so na yi amfani da wannan damar don nuni da Mai Girma Sarkin Musulmi a matsayin misali, in kuma gode wa sarakunanmu da suke nan wajen.”
“Saƙona ga mataimakin gwamnan Sokoto mai sauƙi ne. Sarkin Musulmi ya fi gaban a kira shi Sarkin Sokoto kawai. Shi wata majinga ce da dukkanmu muke buƙatar kare martabarsa don ci gaban ƙasarmu,” in ji Shettima.
Kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasar na zuwa ne jim kaɗan bayan da Shugaban Hukumar Kare Hakkin Musulmai ta Nijeriya MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Sokoto na shirin sauke Sarkin Musulmi.
A makon da ya wuce ne Gwamna Ahmed Aliyu ya gabatar da ƙudurin dokar gyaran dokar masarautun jihar ga majalisar dokokin Sokoto.
Shettima ya ce saƙon nasa na Mataimakin Gwamnan Sokoton ne, wanda shi ne ya halarci taron a madadin Gwamna Aliyu.
A sanarwar da MURIC ta fitar, Akintola ya ce Musulman Nijeriya za su yi watsi da duk wani ƙoƙari na sauke Sarkin Musulmi.
“MURIC na shawartar gwamna da ya yi taka tsantsan kafin ya yi duk abin da yake so. Kujerar Sultan ba ta saratuar gargajiya ba ce kawai, ta addini ce. Ikonsa ya wuce iya Sokoto, yana wakiltar duka Nijeriya ne,” in ji hukumar.