A ranar Asabat din data gabata ne Manoman a jihar Katsina suka koka kan yadda wata bakuwar tsutsa ke ci gaba da lalata gonakinsu na hatsi.
A wata ziyara da gidan talabijin na Channels ya kai wani yanki na gonakin da abin ya shafa a babban birnin jihar, ya gano cewa bakin tsutsotsi na ci gaba da karuwa a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Biyu daga cikin manoman da abin ya shafa, Umar Masoyi da Ahmad Labaran sun ce, karuwar yawan tsutsotsi ya fi yawa a cikin makon, mai yiwuwa saboda karancin ruwan sama yayin da akasarin manoman ke tattara gonakin noma na bana.
Sun ce tsutsotsin sun fi cin masara, gero, da masara.
Don haka ne manoman suka koma feshin maganin kwari da kuma addu’ar Allah ya kawo dauki.