Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) a jiya ta sanar da sabon farashi na naira dubu 100 domin rajista da lasisin sabbin masu shigowa sana’ar tukin keke napep a jihar.

Manajan Daraktan hukumar, Bappa Babba Dan Agundi ya yi ishara da wannan sabon kudin a wani taron manema labarai da aka gudanar a hekwatar hukumar da ke Kano.

Babba Dan Agundi ya ce karin kudin lasisin tukin keke napep daga naira dubu 8 zuwa dubu 100, wani mataki ne na samar da tsafta a kan hanyoyi da kuma rage yawan masu sana’ar.

A cewarsa, galibin masu keke napep na shigowa Kano ne daga jihohi daban-daban tunda sun ga irin alherin da ake samu a Kano da kuma yanayi mai kyau.

Ya yi nuni da cewa wadanda suka yi rajista da naira dubu 8 kuma suna da izinin yin aiki ba sa bukatar jin wani tsoro kasancewar sabon kudin na naira dubu 100 bai shafe su ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: