Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Rt Hon Musa Sulaiman Kadira, ya karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suke yadawa, inda suka bayyana cewa wani bankin ya na binsa bashi.

Idan za’a iya tunawa de wasu kafafen yada labarai sun rawaito yadda wani bankin yake bin Mataimakin Kakakin Majalisar bashin kudade kimanin Naira dubu 849 da 448 wanda har yanzu bai biya ba.

To Sai dai da yake mayar da jawabi mataimakin kakakin Majalisar ya ce wasu gurbatattun mutane ne suka kirkiri labarin domin cimma wata bukatar su ta daban.

Haka kuma ya ce tuni ya tura Lauyoyin sa zuwa Abuja domin ganawa da hukumar Bankin na First Generation Mortgage dake Abuja domin jin wasu karin bayani.

Hon Musa Kadira, ya ce Lauyoyinsa zasu dauki matakin shari’a kan hukumar bankin da kuma kafafen yada labaran da suke yada labaran, biyo bayan yadda suke kokarin kaishi kasa ta kowanne hali.

A cewarsa, an kirkiri labaran ne domin a taba siyasar sa, da kuma mutum cinsa, a kokarin da yake yi wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa domin tabbatar da cewa mutane sun sharbi romon demokradiya.

Kazalika, ya bukaci magoya bayan sa da kuma Al’umma suyi watsi da irin wannan labaran da ake yadawa a wasu daga cikin shafikan sada zumunta. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: