Kicibus Din Yan Shi’a Da Yan Sanda Yayi Muni (HOTUNA)

0 147

A yau ma mabiya Shi’a sun sake gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja, kamar wancan makon, yau ma an sake samun rahoton zazzafar fafatawa tsakaninsu da jami’an tsaro.

A makon da ya gabata ne yan shi’ar suka gudanar da zanga zangar neman tilas a sako shugabansu da gwamnati ke tsare da shi tun shekarar 2015 duk kuwa da kotu ta amince da bayar da belinsa.

Zanga-zangar ta yau dai tayi muni har ma an samu rahoton rasa rai duk kawo yanzu babu alkalumman wadanda suka mutu.

An samu rahoton cinna wuta ga abubuwa da dama da suka jawo lalacewa da asarar dukiya mai yawa, har ma ta kai ga cinnawa wani sashe na ofishin hukumar agajin gaggawa (NEMA) wuta.

Duk da wannan mummunan kicibis tsakanin tsagen biyu da alamu wannan ba zata zamo arangama ta karshe ba duba da yadda tsagen yan Shi’an yayi ikirarin yin duk mai yiyuwa koda zai kai ga sadaukar da rayukan mabiyansu domin ganin an sako shugaban nasu.

Yanzu haka dai tuni aka rawaito yan shi’an sun kashe mataimakin kwamishinan ƴan sanda DCP Usman Umar a yayin zanga-zangar ta yau.

Ibrahim El-Zakzaky

Yayinda suka kuma tsagin gwamnati ke gargadin mabiya Shi’an da kada su sake su harzuka gwamnati.

Dukkan nin bagarorin biyu kawo yanzu sun harzuka, wanda hakan zai iya bayuwa zuwa sake samun wasu zanga-zangar nan gaba.

A ranar 18 ga watan Yuli ne dai mai shari’a Darius Khobo sake daga sauraren karar zuwa 29 ga watan da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: