Kidayar mutanen da cutar korona ta kashe sun wuce miliyan 3

0 146

Hukumar Lafiya ta duniya tace adadin mutanen da cutar korona ta kashe sun zarce miliyan yau yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa duk da allurar rigakafin da ake yiwa jama’a a wasu kasashen Duniya.

Alkaluman Hukumar yace a cikin yan kwanakin da suka gabata ana samun akalla mutane dubu 12 dake mutuwa kowacce rana, abinda ya kara yawan mutanen da annobar ke kashewa.

Wadannan alkaluma na mutane miliyan 3 da suka mutu ya zarce yawan mutanen dake kasashen Jamaica ko Armenia ko kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon yakin da aka gwabza tsakanin Iran da Iraki tsakanin shekarar 1980 zuwa 1988.

Hukumar tace har yanzu cutar bata fara sassautawa ba ganin yadda aka samu sabbin mutanen da suka harbu da ita a jiya juma’a har dubu 829,596 sabanin dubu 731,000 da aka gani a makon jiya.

Birnin Delhi dake India da aka killace mutane a gidajen su a karshen wannan mako ya nuna cewar an samu sabbin mutanen da suka harbu da cutar da yawan su ya kai dubu 234,000 a rana guda, yayin da 1,341 suka mutu.Kasar India ce yanzu ta biyu wajen yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar bayan Amurka, yayin da Brazil ta koma matsayi na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: