Ma’aikatar ruwa kasa ta gina boho bohol mai mafani da hasken rana 14 a kananan hukumomi 14 dake jihar Katsina.

A cewar gwamnatin ta gudanar da wadandan ayyukan ne domin rage matsalar ruwa da ake fuskantar, tare da rage tasirin cutar corona a wuraren da ta samar da wadannan boholan.

Jami’in ma’aikatar na shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan Sanusi Mai-Afu, ya bayyana cewa wannan aiki ne da aka samar domin rage radadin cutar corona, tare da bada tabbacin cewa nan bada daewa ba, za’afara gudanar da wasu ayyukan a Kananan hukumomin da ke Jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, da kuma jihar Kaduna, kasancewar kaso 75 cikin 100 na ruwan da ake amfani da shi a wadannan Jihohin bashi da tsafta.

Guda cikin wadanda ke kula da ayyukan Malam Sanusi Abdullahi Kankara ya bayyana cewa samar da ruwa a wadandan garuruwan ba karamin cigaba bane, saboda ana fuskantar rashin ruwa a koda yaushe.

Wannan aiki ne aka bayyana cewa zai wadatar da kaso 70 cikin 100 na jihar Katsina da ruwa mai tsafta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: