Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya raba zakkar kayan amfanin gona na kimanin naira miliyan 7 a Gundumomin Hakiman Kaugama da Marke da Dakayyawa dake karamar hukumar Kaugama.


A gundumar Kaugama an raba zakkar buhunan gero 77, da na dawa buhu 800 sai buhu 3 na gyada da kuma buhunan wake guda 10 wadanda kudinsu ya kai naira miliyan 2 da dubu dari 7


Sai gundumar Marke, inda kwamitin ya raba buhunan gyada 77 da buhunan gero da dawa 157 da kudinsu ya kai naira miliyan 2 da dubu dari 1.
Hakazalika an raba zakkar buhunan gero 191 a gundumar Dakayyawa da buhu 313 na gyada da shinkafa buhu 9 da kuma tumaki biyu da aka kiyasta kudinsu akan naira miliyan 2 da dubu dari 3.


A jawabin da ya gabatar mataimakin shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia kuma babban limamin Hadejia, Sheik Yusuf Abdurahhaman yace zakka tana tsarkake dukiya baya ga kasancewarta daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci.


Shima sanannen malamain addinin musulunci, Dakta Umar Nasarawa yace zakka wajibi ce ga masu hannu da shuni da kuma manoman da suka noman kayayyakin mafanin gonar da ya kamata a fidda zakka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: