Mahamat Idriss Deby, Dan marigayi shugaban Chadi Idriss Deby

Mahamat Idriss Deby babban jami’i ne a rundunar sojin kasar ta Chadi, kuma daya daga cikin ‘ya’yan marigayi shugaba Deby da ke cikin rundunar sojin kasar.

Tuni dai da rundunar sojin kasar ta rusa gwamnati da majalisar dokoki, jim kadan bayan ba da sanarwar rasuwar shugaba Deby, to amma kuma ta sha alwashin gudanar da sahihin zabe tare da mayar da kasar kan turbar dimokaradiyya nan da watanni 18.

Haka kuma an kafa dokar hana fitar dare a duk fadin kasar, kana kuma aka ba da sanarwar rufe dukkan kan iyakokin kasar.

Mutuwar ta Deby ta zo wa ‘yan kasar a ba zata, kwana daya bayan da aka ayyana marigayin mai shekaru 68 a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda zai ba shi damar wa’adi na 6 a kujerar shugaban kasar.

Deby wanda soja ne, ya kasance shugaban kasar ta Chadi mafi dadewa akan mulki, inda ya soma tun a shekarar 1990 sakamakon wani juyin mulki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: