Majalisar Dokokin jihar Legas,ta bayyana cewa irin su tsohon gwamnan jihar kuma jagoran APC na kasa, Bola Tunubu ne Najeriya ke nema a wannan lokaci.

Kakakin majalisar jihar Mudassiru Obasa, ya shaida cewa taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, abi ne da majalisar ke yi duk shekara.

A wannan shekarar ranar zagayowar haihuwar sa ya fado a daidai majalisar na hutu, shi ya sa sai yanzu majalisar ke nata taya murnar.

Duka ƴan majalisan da suka tofa albarkacin bakin su a lokacin muhawaran a zauren majalisa, sun bayyana cewa Tinubu ne ya fi da ce wa ya jagoranci kasarnan a yanzu.

Sun kara da cewa kwarewarsa da sanin ya kamata sannan kuma jajircewa da yayi wajen mara wa jam’iyyar APC baya har ta kai matsayin da ta ke yanzu a kasar nan, ya isa ace kowa ma ya dawo daga rakiyar wani idan ba shi Tinubun ba.

Yan majalisan sun yi masa fatan Alkhairi da addu’ar Allah ya kara masa Lafiya, tsawon kwana da kuma Allah ya maimaita mana.

Tinubu na daga cikin wadanda ke kan gaba wajen cafke tikitin zama dan takarar kujerar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC a 2023.

Sai dai duk da karin samun karbuwa da yake yi a yankin Kudu Maso Yamma, a Arewacin Najeriya zai iya samun cikas domin wasu da dama bai kwanta musu a rai ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: