Kimanin garuruwa 500 ne na karamar hukumar Shiroro ne yan Boko Haram suka mamaye

0 97

Shugaban Karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja Mista Sulaiman Chukuba, ya ce kimanin garuruwa 500 ne na karamar hukumar sa yan Boko Haram suka mamaye.

Da yake jawabi ga manema labarai a Jiya Shugaban Karamar hukumar Mista Chukuba, ya ce kimanin Mazabu 8 ne suka karkashin yan kungiyar ta Boko Haram.

A cewarsa, wasu daga cikin Mazabun da lamarin ya shafa sun hada da Manta, Gurmana, Bassa-Kokki, Allawa, Kurebe, Kushaka, Kwati, Chukuba da kuma Galadima Kogo.

Mista Suleiman ya ce yan Kungiyar ta Boko Haram sun yiwa mutanen garuruwan tayin basu kudade da kuma Makamai domin tallafawa musu wajen yakar gwamnati.

Haka kuma ya ce karamar hukumar sa ta Shiroro tana daya daga cikin Kananan hukumomin da suka fuskanci hare-haren yan kungiyar Boko Haram lokuta da dama.

Kazalika, ya bukaci gwamnatin Jiha data tarayya su kara yawan adadin Jami’an tsaro domin yakar yan bindigar da suke addabar karamar hukumar ta Shiroro.

A watan Afrilun da ya gabata ne Gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello, ya ce mambobin kungiyar sun kafa tutotun su a karamar hukumar ta Shiroro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: