Kimanin mutane miliyan 3 da dubu 600 za’a yiwa rigakafin cutar Corona a jihar Jigawa a cewar Gwamna Badaru

0 68

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa kafin karshen watan Disamba na shekarar 2021, kimanin mutane Miliyan 3 da dubu 600 ne za’a yiwa rigakafin cutar Corona a Jihar Jigawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da rigakafin cutar na gama gari, wanda aka gudanar a karamar hukumar Kiyawa a ranar Alhamis.

A cewarsa, kimanin mutane dubu 20 da 318 ne aka yi musu gwajin cutar Corona a fadin Jihar nan, inda kuma daga cikin su aka samu mutane 617 da suke dauke da cutar, inda kuma aka samu cutar ta hallaka mutane 17.

Haka kuma, ya ce tun daga watan Maris na shekarar nan ne aka fara gudanar da rigakafin cutar a birnin Dutse, kuma daga wacan lokacin zuwa yanzu mutane dubu 122 ne aka musu rigakafin farko, sai kuma mutane dubu 52 da aka musu rigakafin a zagaye na biyu a fadin Jihar nan.

Kazalika, ya umarci shugabannin kananan hukumomi da na Addinai da kuma masu sarautun gargajiya su ninka kokarin su wajen ganin cewa an yiwa kaso 50 na yan Jihar nan rigakafin cutar akan lokaci.

A jawabinsa, Sakataren Zartarwa na Hukumar Lafiya a Matakin Farko na Kasa, wanda ya samu wakilcin Dr Bashir Mamman ya bayyana cewa ana saran mutane Miliyan 111 ne za’a yiwa rigakafin kafin kashen shekarar 2022 a kasar nan baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: