Kimanin yan Najeriya dubu 330,000 ne suke sansanonin yan gudun hijira a kasashen makotaka – Sadiya Umar Faruok

0 114

Ministar Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk,ta bayyana cewa kimanin yan Najeriya dubu 330,000 ne suke sansanonin yan gudun hijira wanda suke cikin kasashen da suke makotaka da Najeriya.

Ministar ta bayyana hakan ne a lokacin da take Jawabi a wata tattaunawa da aka yi a Chatham House na birnin London domin tattauna kalubalan da suke addabar fannin Jinkai a Kasar nan.

Hajiya Sadiya Umar Farouk ta zayyano Alkaluman kasashen da yan Najeriya suke wanda suka kunshi Chadi mai dubu 16,634, sai Kamaru dubu 118,409 da kuma Jamhuriyar Nijar mai dubu 186,957.

Ministar ta ce Ma’aikatar ta, tana iya bakin kokarin ta wajen ganin cewa ta kaddamar da wasu Daftari 2 wanda zasu tallafawa Ayyukan Jinkai.

Kazalika, ta bukaci karin samun hadin kai domin samar da kayan Agaji a Kasar nan.

Idan za’a iya tunawa Hukumar Samarda Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yan Najeriya Miliyan 3 da dubu 400 ne suke fama da matsalar yunwa a Jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Haka kuma hukumar ta ce kimanin yan gudun hijira Miliyan 4 da dubu 300 ne suka Dogara da abincin tallafi da ake basu a sansanin yan gudun hijirar da suke kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: