Kotu ta yankewa wani Farfesa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari bisa zargin su da laifin buga jabun kudade

0 155

Wata Babbar Kotu dake zamanta a karamar hukumar Birnin Kudu ta nan Jihar Jigawa ta yankewa Farfesa Steve Uchella da Bonafice Afifa Oru hukuncin daurin shekaru 5 a gidan Yari bisa zargin su da laifin yin Jabun kudade.

An gurfanar da masu laifin a gaban alkali mai shari’a Musa Ubale, bisa laifuka guda uku da suka hada da hada baki da aikata laifuka da cin amana da buga jabun kudi.

An fara gurfanar da wadanda ake kara ne a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2018, a gaban kotu kan zargin buga jabun kudi.

Wanda ake tuhumar sun musanta aikata laifuka uku da ake tuhumarsu da su.

Lauyan masu gabatar da kara ya gabatar da shaidu bakwai don bayar da shaida kan laifin.

A saboda haka, alkalin ya ce lauyan masu gabatar da kara ya tabbatar da laifinsu ba tare da shakku ba.

A cewarsa, an sami mutanen biyu da laifin, kuma an yanke musu hukuncin kwashe watanni 3 a gidan Firzin ko kuma biyan tarar Naira dubu 30,000 kowannen su.

Haka kuma Kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 5 bisa Laifin hada baki da aikata laifuka da cin amana da buga jabun kudi, ko kuma su biya tarar Naira dubu 500,000 kowannen su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: