

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya gargadi ‘yan Najeriya da sukauracewa gaisawa da hannu da rungumarjuna bisa fargabar yaduwar cutarcoronavirus.
Aregbesola yayi gargadin ne yayin bikin kaddamar da gidan gyaran hali mai cin mutane dubu 3 a Karshi, Abuja.
Ministan ya shawarci ‘yan Najeriya da suke gaisawa ta hanyar sunkuyar da kai, tare da dafa kirji.

Aregbesola yace cutar coronavirus ta zamaannoba a fadin duniya, inda ya jaddadacewa dole kowa da kowa ya bayar da gudunmawarsa domin tabbatar da cewabata zama babbar matsala anan kasar ba.
Ya kara da cewa dole ‘yan Najeriya su zama masu taka tsantsan da cutar ta coronavirus, tare da yin tsantseni domin dakile ta.